
Sun tattauna akan zaben gwamna da za’a gabatar a jihar da sauran batutuwa
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan jihar Anambra Willie Obiano a fadar shugaban dake Abuja.
Shugaban ya sanar da haka a shafin sa na twitter inda yake tabbatar ma gwamnan cewa gwamnati zata dauki duk mataki na tabbatar da anyi zabe a jihar cikin kwanciyar hankali.
Buhari ya dau alkawari na tabbatar da anyi zaben gwamna wanda za’a yi 18 ga wantan Nuwamba cikin adalci.
Shugaban ya kara ganawa da gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu tare da ministan ma’adinan karkashin kasa Kayode Fayemi a fadar sa ranar talata.
Yayin da yake jawabi ma manema labarai bayan ganawan gwamna Willie Obiano yace shugaban yana son gwamnoni masu ƙwazo irinsa duk da kasancewa jam’iyyar su ba daya bane.
Shima gwamnan ya sha alwashin na cewa jam’iyyar shi APGA baza ta aikata magudi a zaben.
Gwamnan zai yi takara tare da Oseloka Obaze na jam’iiyar PDP, Tony Nwoye na APC na sauran yan takara 34.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment