
Dan majalisar yace yana da damar tsayawa takara domin baya siyasa don amfanin kanshi
Tsohon gwamna kuma dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar zamfara Ahmad Sani Yarima ya bayyana anniyar sa na fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2019 idan shugaba Buhari bai nemi yin tazarce.
Ya sanar da haka ma manema labarai a garin Abuja bayan zaman majalisar yan jam'iyar APC da ya halarta.
Tsohon gwamnan ya sanar cewa zai goyi bayan shugaba Buhari idan har zai fito takara a zaben 2019 amma idan har bai fito ba shi zai fito.
Dan majalisar yace yana da damar tsayawa takara domin baya siyasa don amfanin kanshi.
Har ila yau dai shugaba Buhari bayyana kudirin fitowa takara a zaben 2019.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94

No comments:
Post a Comment