
Majiya sun shaida wa manema labarai cewa yan bindigar sun sace shanu da tumakai.
Yan bindiga sun kai harin gidan gonar Ibrahim Magu shugaban hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC.
Bisa ga rahotannin lamarin ya faru ne a daren ranar talata a gonar dake kauyen Karshi dake wajen garin babban birnin tarayya.
Majiya sun shaida wa manema labarai cewa yan bindigar sun sace shanu da tumakai.
A kwanan baya ne shugaban EFCC ya gama gina gidan da zai zauna a cikin harabar gonar amma bai kai ga tarewa.
Wannan shine karo na biyu da yan bindiga zasu kai hari ga jamÃ'in hukumar EFCC. A wancan karon sun kai harin ne dai dai ofishin hukumar dake nan Wuse a garin Abuja tare da yin harbe-harbe kana suka aje wata wasika mai dauke da barazanar kashe wani jami'in hukumar mai suna Ishaku Sharu.
Karanta labari shugaban ke cewa>> Da taimakon majiya mun gano naira biliyan 29
Shi dai Ibrahim Magu a halin yanzu yana fama da wadanda ake zargi da yi wa tattalin arzikin zagon kasa bisa ga rawan da yake taka wa wajen ganin an hukunta su.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment