A jihar Kaduna: Za'a tallafawa malamai da gidaje kana zasu samu karin albashi na kaso 32.5% - CAMPUS94

Breaking

Entertainment, campus lifestyle, music

Post Top Ad

Post Top Ad

Friday, 2 February 2018

A jihar Kaduna: Za'a tallafawa malamai da gidaje kana zasu samu karin albashi na kaso 32.5%

Gwamna jihar Kaduna Mallam Nasir El-rufai

Duk a shirin tallafawa malamai, gwamnatin jihar zata baiwa ko wani shugaban makaranta gida mai daki uku kana kananan malamai zasu samu gida mai daki biyu.

Malaman makarantun gwamnatin jihar Kaduna zasu samu karin albashi na kaso 32.5%.

Wata sanarwa da kwamishnan ilimi na jihar Ja'afar Sani ya fitar jiya alhamis 1 ga watan febreru, za'a kara kason albashin malamai da 27.5% kana wadanda ke koyarwa a kauyuka zasu samu karin 5%.

Duk a shirin tallafawa malamai, gwamnatin jihar zata baiwa ko wani shugaban makaranta gida mai daki uku kana kananan malamai zasu samu gida mai daki biyu.

*Duk malamin da ya tafi yajin aiki, ya sani cewa iya bakin aikin sa kenan

Bugu da kari za'a bada babura ga malaman domin rage zirga-zirgar kai-kawo wajen aiwatar da aikin su.

Kwamishnan yace an dauki wannan mataki ne domin kara ma malamai kwarraru karfin gwiwa wadanda aka tura kauyuka daban daban.

Ja'afar Sani ya sanar cewa gwamnatin jihar ta sha alwashin bunkasa harkar koyon ilimi a jihar tare da tabbatar da ingantacciyar tsarin koyarwa a duk makarantun dake fadin jihar.

Daga karshe ya sanar cewa gwamnati baza ta lamunta da daukan malamai a makarantun gwamnati bisa tsarin alfarma. Game da malamai 22,000 da gwamnatin jihar ta sallama kwanan baya, kwamishnan yace ana daf da tura wasu sabbin malamai 10,000 zuwa makarantu daban daban dake kananan hukumi 23 na jihar.

posted by Campus94

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here